Bangaren kas ada kasa, dubban mutane ne suka gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a kasar Jordan domin nuna rashin amincewarsu sa lon mulkin kasar, tare da yin kira da akawo karshen cin hanci da rashawa acikin harkokin mulki a kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, an gudanar da wannan zanga-zanga ne da taken cewa “kada ku yaudare mu” bayan kammala sallar Juma’a a gaban babban masallacin A’azam Husaini da ke tsakiyar birnin Amman fadar mulkin kasar.
An gudanar da wannan zanga-zanga bayan da kungiyoyi da jamiyun siyasa masu adawa na kasar suka yi kira ga dukaknin mutane da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin nuna rashin gamsuwarsu da yadda ake tafiyar da harkokin siyasa da mulki a kasar wanda ya yi hannun riga da abin da mutane suke bukata.
Masu jerin gwanon sun bukaci da a rusa majalisar dokokin kasar, bisa abin da suke kira da cewa ta zama wani dandali na cin hanci da rashawa maimakon gudanar da ayyuka na wakiltar al’ummar kasar da suka zabe su da kuri’a.
Kwanakin baya ne majalisar dokokin kasar ta amince da wani daftarin kudiri da yake yin kira da a ladabtar da duk wanda aka asamu da laifin hanci da rashawa a cikin aikinsa, tare da cinsa tara ta makudan kudade.
870352