Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin yanar gizo na al-alam cewa gidajen talabijin fitattu a duniya guda goma sha biyu ne suka watsa jawabin da jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran ya gabatar a taron nuna goyon baya ga al’ummar palastinu, wanda ake gudanarwa akaro na biyar a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran.
Matsalar Palasdinawa, wani babban al'amari ne da kasashen musulmin baki daya ke dauka da muhimmanci''. Da wadannan kalamai ne jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullahil Uzma Sayyed Ali Khemenei ya soma jawabinsa na buda taro karo na 5 dan nuna goyon baya ga gwagwarmayar Intifada ta al'ummar Palasdinu da aka soma a jiya asabar a nan birnin Tehran.
A lokacin da yake yin tsokaci dangane da manyan dalilan da suka haifar da samuwar kungiyoyin gwargwarmaya da ke dauke da makamai a Palasdinu a daidai lokacin da wasu ke yin kira da a gudanar da tattaunawa, jagoran ya ce yin amfani da hanyoyi na yaudara cikinsu kuwa har da kulla yarjejeniyar munafunci ta Camp David abubuwa ne da suka taimaka matuka domin samar da irin wadannan kungiyoyi a Palasdinu. Ayatullahi Sayyed Ali Khemenei ya ce abubuwan da suka faru kafin da kuma bayan kulla wannan yarjejeniya ta Camp David sun wajabta wa Palasdinawa ma'abota 'yanci daukar makamai dan kwato kasarsu daga hannun 'yan mamaya.
Jagoran ya ce akwai alamun samun nasara da kuma kawo karshen wannan mamaya ta Yahudawan Sahyuniyya, kuma hakan na kara tabbata idan aka yi la'akari da galabar da 'yan gwagwarmayar na kasar Labanan suka samu a kan yahudawa Sahyuniyya a shekara ta 2006, da kuma yadda al'ummar Gaza suka tsaya domin kare kasarsu a lokacin da yahudawan suka kaddamar da yaki a kansu a shekara ta 2009.
870836