IQNA

16:12 - October 06, 2011
Lambar Labari: 2199988

Za A Kafa Bankin Musulunci Na Kasa Da Kasa Na Biyu A Kasar Oman

Bangaren kasa da kasa, za a kafa bankin musulunci na biyu a matsayi na kasa da kasa a birnin Maskat fadar mulkin kasar Oman wanda aka sanya ma suna Al’iz tare da amincewar gwamnatin kasar kan hakan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar latabijin din Aljazeera cewa, a ci gab ada bunkasa harkokin banki da kasuwanci a kasashen musulmi za a kafa bankin musulunci na biyu a matsayi na kasa da kasa a birnin Maskat fadar mulkin kasar Oman wanda aka sanya ma suna Al’iz tare da amincewar gwamnatin kasar kan hakan kamar yadda majiyoyin suka tabbatar.
Babban darakta a bangaren gudanarwa a babban bankin kasar Oman Hamud Sanjur shi ne ya sanar da hakan a wata zantawa da ta hada shi da manema labarai, inda ya sheda cewa kafa wannan banki na da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin kasar, da kuma bunsa lamurra ta fuskacin harkokin banki.
Kafa bankin musulunci na biyu a matsayi na kasa da kasa a birnin Maskat fadar mulkin kasar Oman wanda aka sanya ma suna Al’iz tare da amincewar gwamnatin kasar kan hakan, na daga cikin muhimman ayyuklan da ma’aikatar harkokin kudi da bunkasa kasuwanci ta kasar ta mayar da hankali kansu.
873931

captcha