IQNA

Akalla Mutane 13 Ne Suka Yi Shahada A Kasar Pakistan Sakamakon Harin Ta’addanci

17:05 - October 06, 2011
Lambar Labari: 2199999
Bangaren siyasa da zamantakewa, mutane 13 ne aka tabbatar da sun rasa rayukansu sakamakon wani harin ta’addanci da wasu ‘yan ta’adda masu akidar kafirta musulmi suka kai kansu da suke samun goyon baya daga kasar Saudiyya domin kara rarraba kan al’ummi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Zeemukl Maktib cewa, mutane 13 ne aka tabbatar da sun rasa rayukansu sakamakon wani harin ta’addanci da wasu ‘yan ta’adda masu akidar kafirta musulmi suka kai kansu da suke samun goyon baya daga kasar Saudiyya domin kara rarraba kan al’ummi kamar dai yadda shi ne manufar ‘yan mulkin mallaka da gwamnatin Saudiyya take wakilta acikin kasashen larabawa da na musulmi.
A cikin kwanakin bayan nan an yi sabbin dokokin fada da ta'addanci da su ka kunshi daurin shekaru goma a gidan kurkuku ga duk wanda ya yi shakku akan matsayin sarki da kuma yarima mai jiran gado. Kuma dokokin sun bada dama ga jami'an tsaro da su kama da daure mutane ba tare da shari'a ba har tsawon shekara guda. Za kuma a iya tsare mutumin da ake yi wa zargi da ta'addanci ba tare da shari'a ba na tsawon kawnaki 120 shi kadai a cikin daki a wakafi.

Basim Alim wanda lauya ne mai zaman kansa a cikin Saudiyya ya fadi cewa, wadannan dokokin ba su da alaka da ayyukan ta'addanci, an yi su ne saboda murkushe duk wani yunkuri na son kawo sauyi.
Wannan matakin na mahukuntan Saudiyya ya biyo bayan yunkurin da mutanen kasar su ka rika yi ne daidai da sauran 'yan'uwansu larabawa na neman shimfida adalci acikin kasashensu. Wannan shi ne abinda ya tada hankalin mahukuntan kasar ya sa su daukar matakai masu tsanani akan 'yan kasa. Sai dai wannan irin mataki ya tabbatar da cewa baya haifar da Da mai ido kamar yadda ya bayyana a cikin kasashe da dama na larabawa.
873679

captcha