Kamfanin dilalncin labaran iqna ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na na tashar talabijin din Al-alam cewa, majalisar malaman addinin muslunci a palastinu ta yi na'am da matsayin jagoran juyin juya halin Musulunci a kasar Iran dangane da yadda ya kamata a dawo da dukaknin hakkokin palastinawa da haramtacciyar kasar Isra'ila ta mamaye kuma take ci gaba da mamayewa a halin yanzu.
A bangare guda kuma rahoton ya ce Wakilin kasar Masar a majalisar dinkin duniya ya mayar da martani kan kiran da pira ministan Isra'ila ya yi da ke neman palastinawa su koma kan teburin tattaunawa tare da Isra'ila ba tare da bata lokaci ba.
Kamfanin dillancin labaran Qods net ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban daliban jami'ar Colombia da ke birnin New York na kasar Amurka, wakilin kasar Masar a majalisar dinkin duniya Majid Abdulfattah ya yi dirar mikiya kan kan pira ministan Binyamin Natanyaho, inda ya ce har kullum tana yawo da hankulan al'ummomin duniya ne kan batun sulhu tsakaninta da palastinawa, ya ce Masar za ta ci gaba da fadi tashin ganin al'ummar palastinu ta samu kasarta mai cin gishin kanta kamar sauran al'ummomi na duniya.
A 'yan kwanakin da suka gabata ne palastinawa suka gabatar da bukatar samun kasar kansu mai cikakken wakilci a majalisar dinkin duniya, inda akasarin kasashen duniya suka yi na'am da hakan, amma Amurka da ke da hakkin hawa kujerar naki a kwamitin tsaro, tare da wasu 'yan tsiraru daga cikin kasashen turai suka ki amincewa da hakan. 874949