Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Ayatullahi Isa Kasim limamin juma'a a kasar Bahrain a ranar juma'ar da ta gabata sha biyar ga watan Mehir shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya jaddada cewa: matsalar al'ummomin larabawa a yau ta shafi mahukumata da gwamnatocin da suke jagorancin kasashensu karkashin umarnin yan mulkin mallaka tare da take hakkin al'ummominsu matukar manufarsu ta yi karo da ta kasashen yammacin Turai.Wannan malami jagoran yan shi'a a kasar ta Bahrain ya ja kunnan shugabanni da mahukumata da gwamnatocin kasashen Larabawa da su komo daga rakiyar yan mulkin mallaka na yammacin Turai da yin la'akari da bukatun al'ummominsu a maimakon su maida hankali kan bukatun kasashen yammacin Turai yan mulkin mallaka da danniya domin manufar kasashen yammaci yada fasadi na addini da matsalolin a cikin kasashen musulmi.
875436