Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Abdulrahman Wabili daya daga cikin fitattun marubuta a kasar Saudiyya ya yi kira da safke limamin masallacin manzon Allah da ke birin madina mai alfarma, saboda rashin dacewarsa da ya zama limamin wannan masallaci mai daraja domin kuwa abin da yake ya yi hannun riga da koyarwar manzo.
Marubucin wanda ya yi suna a cikin marubutan jaridar Al-watan ta kasar saudiyya ya ce, kafirta mabiya mazhabar shi'a da Huzaifi ya yi ba koyarwa b ace irin ta sunnar manzon Allah (SAW) saboda haka ya kamata tun wuri mahukuntan kasar Saudiyya su dauki matakin taka masa burki ta hanyar safke daga limancin masallacin manzon Allah.
A ranar juma'ar da ta gabata ce Huzaifi wanda daya ne daga cikin malaman wahabiyawan Saudiyya, kuma limamin masallacin ma'aiki (SAW) ya yi wani furuci mai matukar hadari, inda ya fitar da mabiya tafarkin Ahlul bait daga addinin muslunci.
Malaman mabiya tafarkin shi'a kasar Saudiyya da sauran kasashen duniya sun yi kakkausar suka kan wannan danyen aiki da malamin wahabiyawan ya yi, wanda ga dukkanin alamu wani shiri na jefa kasar cikin rikicin addini daga makiya Musulunci.
876145