Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dilalncin labaran reauters cewa, majalisar sojojin kasar Masar ta gargadi 'yan siyasa da su guji rera duk wani take da yake da dangantaka da addini a lokacin da suke gudanar da kamfe na siyasa a kasar, domin kauce ma cakuda siyasa da addini a zabukan da za a gudanar a kasar a cikin 'yan lokuta masu zuwa.
Gwamnatin sojoji a kasar Masar ta bada sanarwan kafa dokar hana yawon dare a wasu yankuna na babban birnin kasar Alkahira, daga karfe 2.00 na dare zuwa karfe 7;00 na safe.
Gwamnatin ta dau wannan matakin ne bayan karawan da jami'an tsaron kasar suka yi da kiristoci yan darikar Coptic wadanda suke zanga zangar neman gwamnati sojojin kasar ta sake ginin wani chocin da aka rusa masu a cikin watanni da suka gabata.
Masu zanga zangar sun yi cicinrindo a gaban ginin wani gidan televisin mallakar gwamnati a unguwar Mespero na birnin, suna bayyana bukatunsu ga gwamnatin kasar da babbam murya.
Priministan kasar Masar Essam Sharaf ya bayyana cewa masu zanga zanagar suna dauke da makamai, kuma rikicin ba tsakanin musulmi da kirista bane.
Wasu kafafen yada labaru dai sun bayyana cewa jami'an tsaro sun yi amfani da albarusai na gaskiya kan masu zanga zangar, kuma akalla mutane biyu sun rasa rayukansu, sannan wasu da dama kuma suka ji rauni.
877126