Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci tai ran ne ya watsa rahoton cewa : sabon firaministan kasar Jodan yayi alkawali da bada tabbatcin cewa: a sabuwar gwamnatin da zai kafa zai sanya yayan kungiyar Ikhwalun musulunci da ke kasar ta Jodan a wani mataki irinsa na farko da ake ganin bay a rasa nasaba da sauyin da ake gani a yau a kasashen yankin.Aun Alkhasawina firaministan kasar Jodan a ranar ashirin da biyar ga watan Mehr na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya bayan marabis din Ma'aruf Albakhit ,Abdallah na biyu sarkin Jodan ya nada shi inda a gaban manema labarai ya bayyana cewa ; yana fatar Ikhwanul Musulim su amsa wannan bukata ta ganin sun shiga a cikin sabuwar gwamnatin da zai kafa da amincewa da sharadinsu.
882043