IQNA

13:51 - October 20, 2011
Lambar Labari: 2208441

Yan Jami'a Za Su Taru Don Yin Allah Wadai Da Zargin Baya Bayan Nan Kan Iran

Bangaren siyasa: yan jami'a za su tari a gabana ofishin jakadancin kasar Suiziland da ke kula da harkokin Amerika a nan Iran domin yin Allah wadai na zargin baya-bayan nan da Amerika ta yi wa jamhuriyar musulunci ta Iran na kitsa wani shiri na yin kisan gilla kan jakadan kasar Saudiya da ke Amerika.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: yan jami'a za su tari a gabana ofishin jakadancin kasar Suiziland da ke kula da harkokin Amerika a nan Iran domin yin Allah wadai na zargin baya-bayan nan da Amerika ta yi wa jamhuriyar musulunci ta Iran na kitsa wani shiri na yin kisan gilla kan jakadan kasar Saudiya da ke Amerika.Davud Gudarzi mukaddashin bangaren siyasa a hukumar zartarwa ta dakarun yan jami'a a kasar Iran ya bayyana cewa: wannan taron sun shirya shi ne domin isar da sako da martini mai girma kan Amerika da kwawayenta da suka kitsa da amincewa da wannan zargi domin cimma wata manufa ta su ta siyasa a yankin da kuma kokarin shafawa Jamhuriyar musulunci ta Iran kashin kaji a tsakanin takwarorinta na duniya da hakan ba zai haifi da mai ido bag a manyan kasashen na duniya.

883266
captcha