Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin dil Almanar cewa, shugaban kwamitin bayar da fatawoyin musulunci a kasar Rasha ya yaba da gwagwarmayar kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon musamman ma jagoran kungiyar Sayyid Hassan nasrullah wanda ya bayar da kyakyawan misali wajen nuna kishi ga al’ummarsa.
Sheikh Ainuddin ya bayyan ahakan ne a lokacin da yake gaanawa da tawagar ‘yan majalisar dokokin kasar Lebanon bangaren kungiyar hizbullah, da ke gudanar da ziyara ta kwani uku a kasar Rasha, inda tawagar ta gana da manyan jami’an gwamnatin kasar Rasha.
shugaban kwamitin bayar da fatawoyin musulunci a kasar Rasha ya yaba da gwagwarmayar kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon ne saboda darsin da ta koyawa yahudawan sahyuniya da suke yi wa sauan musulmin duniya kallon hadarin kaji, inda hizbullah ta zubar da girman kansu kasa warwas.
Babbar manufar ziyarar dai ita ce ganawa da bangaren Rasha kan yadda bangrorin biyu suke kallon lamurran da suke gudana a yankin gabas ta tsakiya, tare da nuna rashin amincewa da shigar shugula ta kasashen turai.
883945