Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar palastinul yaum cewa, palastinawan da suka fito daga kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila za su tafi kasa mai tsarki domin safke farali na aikin haji a wannan shekara, kamar dai yadda majiyoyin gwamnatin palastinu a gaza ta sanar a cikin wani baynai da ta fitar kan hakan.
A bangare guda kuma masana na tofa albarkacin bakinsu kan wannan musayar fursunoni, shekaru biyar haramtacciyar Kasar Isra'ila ta yi tana son 'yanto da sojanta "Gil'ad Shalit" daga hannun 'yan gwagwarmayar palasdinu a yankin Gaza amma ba ta sami nasara ba, abinda ya sa ta mika kai ga sharuddan da 'yan gwagwarmaya su ka kafa na musayar fursunonin palasdinawa da sojan nata.
A jiya talata ne dai manyan motocin safa-safa da su ke dauke da fursunonin da aka saki su ka isa Masar ta mashigar Rafah. A daidai wannan lokacin ne kuwa haramtacciyar Kasar Isra'ila ta sanar da karbar sojanta Shalit daga hannun Misrawa da 'yan gwagwarmaya su ka mika shi. Jami'an leken asirin Masar ne dai su ka sanya idanu akan yadda musayar fursunonin ta rika gudana da kuma karbarsu daga hannun h.k. Isra'ila da kuma palasdinawa.
Bugu da kari jami'an leken asirin masar din su ka bincika sunayen wadanda aka fitar da sunayensu domin ganin ko sun dace da wadanda aka saki din daga kurkukun Nakab.
A cikin Masar kuwa tawagar kungiyar Hamas a karkashin jagorancin Musa Abu Marzuk ce ta karbi fursunonin a bakin mashigar Rafah.
883940