Bangaren kasa da kasa: wani gungu na wahabiyawa a kasar Masar a daren ranar daya ga watan Aban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya sun kai wa masallacin Tauhidi a lardin Dakhaliya na kasar Masar inda suka kara kofa da tagogin wannan masallaci kuma guri mai tsarki na Ibadar musulmi.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; wani gungu na wahabiyawa a kasar Masar a daren ranar daya ga watan Aban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya sun kai wa masallacin Tauhidi a lardin Dakhaliya na kasar Masar inda suka kara kofa da tagogin wannan masallaci kuma guri mai tsarki na Ibadar musulmi.An nakalto daga jaridar Aldastur da aka bugawa a kasar ta Masar na cewa; mazauna kewayen kauyen Basat da ke karkashin garin Dalkha a lardin Dakhaliya na Masar sun bayyana cewa; wani gungun mahabiyawa ne ya kai hari kan amasallaci a wani mummunan mataki na kaita hurumin gurin ibadar musulmi da kuma haddasa fitina a tsakanin musulmi a wannan kasa ta Masar.
886259