Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na Myfox NY cewa, yanzu haka an bude wani taro na raya al'adun muslunci a karo na goma sha biyar a babban dakin ajiye kayan tarihin nan da ke birnin New York na kasar Amurka tare da halartar wasu daga cikin manyan jami'an ofishin magajin gari na birnin ad suke fatan ganin an samu fahimtar juna tsakanin musulmi da wadanda ba musulmi ba.
Birnin New York dai shi ne babban birnin ta fuskanci harkokin kasuwanci da yada al'adu a kasar Amurka, tare da hada-hada ta kasa da kasa, kuma wannan cibiya ta kwashe tsawon shekaru kimanin gom asha biyar tana gudanar da irin wannan shiri, wanda ke samun karbuwa daga al'ummar kasar masu son zama lafiya daga cikinsu.
Bude taro na raya al'adun muslunci a karo na goma sha biyar a babban dakin ajiye kayan tarihin nan da ke birnin New York na kasar Amurka tare da halartar wasu daga cikin manyan jami'an ofishin magajin gari na birnin, na daga cikin muhimman ayyukan wannan cibiya.
886882