IQNA

Bangaren kasa da kasa: wani gungu na al'ummar libiya a garin Bangazi sun gudanar da wata gagaramar zanga-zanga inda suke bukatar a gudanar da shari'ar musulunci da tsari irin na addini a cikin kundin tsarin mulkin kasar.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: wani gungu na al'ummar libiya a garin Bangazi sun gudanar da wata gagaramar zanga-zanga inda suke bukatar a gudanar da shari'ar musulunci da tsari irin na addini a cikin kundin tsarin mulkin kasar.A ranar shidda ga watan Aban ne shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya bayan sun taru a dandalin Tahri da ke tsakiyar birnin na Bangazi sun jaddada cewa; kur'ani shi ne tushe da asali na rayuwa saboda haka sabbin dokokin tsarin mulkin kasar Libiya dole ne ya kasance karkashin tsari da shari'ar musulunci.Ahmad Almargribi limamin daya daga cikin limamai a birnin Bangazi ya bayyana cewa; mu musulmi ne da muke rayuwa daya daga cikin kasashen musulmi kuma mun yi amanna da dokokin shari'ar musulunci.


888832