Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakaltodaga shafin sadarwa na yanar gizo na Euro Islam cewa, ana shirin gudanar da wani zaman taro a mataki na kasa da kasa mai taken musulunci a kasar Australia da kuma nahiyar turai wanda zai gudana a babban dakin gudanar da taruka na jami’ar birnin Canbra na kasar Australia.
Tun kafin wannan lokacin dai an saba gudanar da irin wannan taro a kowace shekara, da nufin tatatunawa kan muhimman batutuwa da suke da dangataka da wasu daga cikin abubuwan da ake da fahimtar juna a knsu tsakanin al’ummomin muslumi da kuma wadanda ba musulmi ba na kasashen Australia da kuma nahiyar turai.
Ko shakka babu gudanar da zaman taro a mataki na kasa da kasa mai taken musulunci a kasar Australia da kuma nahiyar turai wanda zai gudana a babban dakin gudanar da taruka na jami’ar birnin Canbra, na da matukar muhimmanci wajen kara kusanto da fahimta tsakanin dukaknin bangarori.
888965