IQNA

UNESCO zata Baiwa Palastinu Damar Zama Mambanta Ta Dindin

17:42 - October 30, 2011
Lambar Labari: 2214567
Bangaren kasa da kasa, hukumar kula da harkokin bunkasa ilimi da al’adu ta majalisar dinkin duniya UNESCO za ta bayar da dama ga palastinu ta zama mamba ta dindin a cikin hukumar duk kuwa da nuna rashin amincewar Amurka da wasu daga cikin kasashen yammacin turai.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-bayan ta kasar hadaddiyar daular larabawa cewa, hukumar kula da harkokin bunkasa ilimi da al’adu ta majalisar dinkin duniya UNESCO za ta bayar da dama ga palastinu ta zama mamba ta dindin a cikin hukumar duk kuwa da nuna rashin amincewar Amurka da wasu daga cikin kasashen yammacin turai da kuma haramtacciyar kasar Isra’ila.
Rahoton ya ce hukumar ta dauki wannan matakin ne bayan amincewar kusan dukkanin mambobinta in banda wadanda aka ambata, wadanda kuma su ne suka ki amincewa palastinu ta zama mamba a majalisar dinikin duniya a matsayin kasa mai cin gishin kanta, lamarin da ya kara fito da matsayinsu kowa ya gansu a duniya.
A jibi ne dai ake sa ran hukumar kula da harkokin bunkasa ilimi da al’adu ta majalisar dinkin duniya UNESCO za ta bayar da dama ga palastinu ta zama mamba ta dindin a cikin hukumar duk kuwa da nuna rashin amincewar Amurka da wasu daga cikin kasashen yammacin turai masu adawa da musulmi da larabawa.
889091



captcha