IQNA

Ganawa Tsakanin Kungiyar Matan Masar Da Sakataren Hukumar Kusanci Tsakanin Musulmi

13:03 - November 02, 2011
Lambar Labari: 2216419
Bangaren siyasa da zamantakewa;wata tawaga ta matan Masar sun yi wata ganawa da Ayatullahi Taskhiri babban sakataren hukumar kara kusanci da dangantaka a tsakanin mazhabobi na musulunci da kuma Tabra'I mukaddashin cibiyar hulda ta kasa da kasa inda suka tattauna kan lamurra da matsaloli iri daban daban da suke addabar musulmi.






Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa: wata tawaga ta matan Masar sun yi wata ganawa da Ayatullahi Taskhiri babban sakataren hukumar kara kusanci da dangantaka a tsakanin mazhabobi na musulunci da kuma Tabra'I mukaddashin cibiyar hulda ta kasa da kasa inda suka tattauna kan lamurra da matsaloli iri daban daban da suke addabar musulmi.Sun tattauwa hanyoyin da ya kamata a bi domin magance matsalolin da ke addabar musulmi a yau da kuma hanyoyin yadawa da kuma bunkasa al'adun musulmi a kasashensu uwa uba yada addinin musulunci da kara kusanci da fahimtar juna a tsakanin musulmi masu bin mazhabobi mabanbanta a kasashe daban daban.har ila yau sun bayyana cewa wannan hukumar ta kara kusanci da fahimtar juna a tsakanin mazhabobi bay a nufin yin katsalanda a harkokin wasu mazhabobin illa fahimtar juna bisa la'akari da kowa ya rike akidarsa da sabanin fahimtarsa amma a fahimci hadafinmu daya ne shi ne musulunci.




891197

captcha