IQNA

21:32 - November 17, 2011
Lambar Labari: 2223695

Kyamar Musulmi Da Musulunci Na Karuwa A Kasar Amurka

Bangaren kasa da kasa, wata kididdiga da hukumar 'yan sanda mai binciken manyan laifuka a kasar Amurka ta FBI ta fitar na nuni da cewa kyamar musulmi da addinin muslunci ya karu matuka a tsakanin al'ummomin kasar Amurka.




Kamfanin diallcnin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Nation cewa, kididdiga da hukumar 'yan sanda mai binciken manyan laifuka a kasar Amurka ta FBI ta fitar na nuni da cewa kyamar musulmi da addinin muslunci ya karu matuka a tsakanin al'ummomin kasar Amurka musamman ma a cikin 'yan shekarun baya-bayan nan.

A bangare guda kuma daruruwan masu zanga-zangar a birnin Washington na kasar Amurka ne suka yi tattaki har zuwa fadar White House a marecen jiya, inda kuma suka bukaci shugabar kasar Barack Obama da ya shiga sahun masu zanga-zangar domin kawo gyara ga salon jarin hujja wanda ke ci gaba da haifar da dimbin matsaloli ga al'ummar kasar.

Birnin Washington dai na daya daga cikin garuruwan da masu zanga-zangar suka mamaye a tsawon watanni biyu, inda suka kafa tantuna a kusa da fadar shugaban kasar da kuma wasu muhimman gine-ginen gwamnati, suna masu yin kira ga Obama da ya shigo cikin wannan gwagwarmaya ta hanyar yin maci a kan titunan da kuma shafe wa jama'ar kasar hawayensu.

Sa'o'i kadan kafin wannan jerin gwano na al'umma zuwa fadar White House, a can kuwa birnin New York wanda shi ne matattarar manyan cibiyoyi na 'yan jari hujja, 'yan sanda ne suka yi amfani da karfi dan tarwatsa jama'a tare kuma da kwashe tantunan da suka kafa a kan tituna, kuma rahotanni sun ce akalla mutane dari biyu ne aka kama a birnin na New York fadar mulkin kasar.

899464







captcha