Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-anba cewa, ana shirin bude wani shafi na sadarwa kan harkokin addinin Musulunci a da zai rika magana da yaruka goma sha biyar a kasar turkiya da za a kafa ofishinsa abirnin Istanbul.
A wani labarin kuma gwamnatin kasar Syria ta ce ba za ta halarci taron hadin gwiwa da kungiyar kasashen laraba da kuma Turkiyya za su yi dan tattauna batutuwan da suka shafi kasar ta Syria da kuma sauran kasashen larabawa wanda aka shirya gudanarwa a wannan laraba a birnin Rabat na kasar Maroko ba.
A wata sanarwa da ta fitar a cikin daren jiya, gwamnatin Syria ta ce bayan da kungiyar ta larabawa ta dakatar da ita daga cikinta a ranar asabar da ta gabata, Syria ta yanke shawarar kin halartar wannan taro na birnin Rabat wanda ta ce an tsara shi ne da nufin cutar da kasar.
Sanarwar ta gwamnatin Syria ta ci gaba da cewa, a matsayin kasar da ke da akidar kare manufofin kirkiro wannan kungiyar ta kasashen laraba kamar samar da hadin kai, da kuma kare martabar laraba a duk inda suka a duniya, ta la'akari da yadda wasu ke neman mayar da kungiyar mai kare manufofin wasu kasashen na daban, to babu hujjar Syriar ta halarci wannan taro na yau.
899312