IQNA

21:31 - November 17, 2011
Lambar Labari: 2223869

Mai Fatawa Na Saudiyya Ya Halasta Yin Magani Da Kur'ani Ga Wadanda Ba Musulmi Ba

Bangaren kasa da kasa, wani daya daga cikin masu bayar da fatawa a kasar Saudiyya ya halasta yin amfani da kur'ani mia tsarki domin magani ga wadanda ba musulmi, bisa dalilin cewa cewa ceto ga dukkanin talikai kamar yadda yadda nassin zaihirin aya ya nuna.




Kamfanin dillancin labaran iqna ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum Al-sabi cewa, daya daga cikin masu bayar da fatawa a kasar Saudiyya ya halasta yin amfani da kur'ani mia tsarki domin magani ga wadanda ba musulmi, bisa dalilin cewa cewa ceto ga dukkanin talikai kamar yadda yadda nassin zaihirin aya ya nuna ba tare da kawo tawili ba.

Wani labarin kuma yana cewa, har ila yau wakilin na Iran ya sake jaddada cewa babu hannu gwamnatin Iran ko kuma wata cibiya da take da alaka da ita cikin wannan tuhuma inda ya ce bakar farfagandar da Amurka take yadawa kan Iran da kuma gabatar da irin wannan tuhuma maras tushe wani abu ne da ke nuni da bakar aniyar da jami'an Amurkan suke da ita kan Iran.
A watan Oktoban da ya gabata ne Amurka ta sanar da cewa ta kama wasu mutane wadanda wai suke da alaka da Iran da suke kokarin kashe jakadan Saudiyya a Amurka Adil al-Jubair. Shi dai wannan mutumin Ba'amurke amma dan asalin kasar Iran da ake tuhuma ya musanta wannan zargi a lokacin da aka gabatar da shi a gaban kotu.
Masana dai suna ganin wannan tuhuma ta Amurka ta saba wa hankali sannan kuma babu wani amfani na siyasa da Iran za ta samu idan ta kashe jakadan Saudiyya wanda ba a bakin komai ya ke ba a fagen siyasar kasar Saudiyyan, don haka suke ganin gabatar da wannan batu wani kokari ne kawai da Amurka take yi na haifar da fitina a tsakanin kasashen Iran da Saudiyya don sake rarraba kan al'ummar musulmi na duniya don su sami damar cimma manufofin da suke da su a wannan yanki da kuma sauran kasashen musulmi.
899255

captcha