Kamfanin dillancin Labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a karo na biyu za a gudanar da taron kasa da kasa na koyar da alkalancin karatun kur'ani musamman a daidai lokacin gudanar da gasar karatun kur'ani karo na talatin da uku ta kasa da kasa ta harda da tajwidi da kuma tafsirin kur'ani a kasar saudiya a cikin watan Muharram. Daga cikin wadanda za su halarci wannan horo na alkalancin kur'ani a kasar Saudiya shidda sun fito ne daga kasar Saudiya yayin da wasu sha uku suka fito daga kasashen goma sha biyu na duniya domin halartar wannan horo a daidai lokacin gudanar da gasar karatun kur'ani mai girma da aka saba gudanarwa a kowa ce shekara a kasar ta Saudiya a gasa ta kasa da kasa irin mafi girma a duniya ta fuskar karatun kur'ani da harda.
901342