Kamfanin dilalncin labaran iqna yahabarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an gudanar da gagarumar zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar birnin Qods da kuma yin Allawadai da yahudawan sahyuniya kan yunkurin da suke yi na rushe masallacin Qods mai alfarma a cikin ‘yan lokutan nan.
Al'ummar kasar Jordan sun yi zanga-zanga a yau juma'a domin yin Allah wadai da siyasar nuna wariya ta haramtacciyar Kasar Isra'ila, dubban masu zanga-zangar ne su ka amsa kiran kungiyoyin jam'iyyun musulunci na fitowa a yau juma'a saboda da yin zanga-zangar nuna goyon bayansu ga gwagwarmayar al'ummar palasdinu da kuma yin tir da siyasar haramtacciyar Kasar Isra'ila.
Wani jagora na kungiyar 'yanuwa musulmi a kasar ta Jordan, Ibrahim al-Kaylani da ya gabatar da jawabi a wurin zanga-zangar ya bayyana wajabcin 'yanto da palasdinu bakin dayanta daga mamayar 'yan sahayoniya.
904821