Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na OIC cewa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Akmaluddin Ihsan ya nuna matukar damuwa kan halin da ake ciki yanzu haka a kasar Masar musamman ma kisan kiyashin da ake yi kan fararen hula masu neman sauyi a kasar bayan da suka fahimci cewa har yanzu akwai sauran runa a kaba.
Saboda kwantar da hankalin jama'a da rage boren da suke yi mata, majalisar mulkin sojan kasar Masar ta amince da murabus din da Isam Sharaf ya yi daga mukamin piramonista kuma ta nada Kamal al-Janzuri a madadinsa. Al-Janzuri dan shekaru 78 da haifuwa, wanda kuma ya ke dauke da takardar shaidar digiri na uku a fannin tattalin arziki, ya taba zama piraministan kasar Masar a zamanin hambararren shugaban kasar Husni Muibarak.
Bayan da boren masu zanga zanga a Masar ya tsananta har ma ya lashe kimanin rayuka 40, dole ta sa Isam Sharaf ya ajiye aikinsa na piraminista, amma da farko majalisar mulkin soja bata karbi murabus din da ya yi ba. Daga baya, da majalisar soja ta ga ba sarki sai Allah, sai ta ce ta amince da murabus din gwamanatin Isam Sharaf saboda amsa bukatun alumma wadanda su ne suka nemi Isam Sharaf ya sauka. Amma manazarta harkokin kasar ta Masar suna ganin cewa amincewa da saukar Isam Sharaf da kuma nada Kamal al-Janzuri wani kokari ne na sassauta boren da jamaa suke yi wa sojojin.
Da akwai suka mai yawa da ake yi wa zabar al-Janzuri a matsayin sabon piraministan kasar Masar. Kamal al-Janzuri dai sanannen mutum ga matasan kasar Masar kuma jamaa sun san abubuwan da ya aikata a fagen siyasar kasar sarai. Masu adawa da al-Janzuri suna zarginsa da laifuka masu yawa a zamanin da ya kasance piraminista, cikinsu kuwa har da yin almundahana da dukiyar alumma, da halayya irin ta kama karya, da saba wa kundin tsarin mulki, da kuma rashin iya gudanar da harkar shugabanci.
Masu juyin juya halin Masar dai sun yi imanin cewa Kamal al-Janzuri ba abinda zai iya yi banda zaratar da umurnin majalisar ta sosoji kamar dai yanda Isam Sharaf ya kasa samun yancin gudanar da wani abu idan ba da izinin majalisar ta soja ba. 904828