IQNA

Jamhuriyar Musulunci Ta Hanayr Dogaro Da kai Ta Karya Lagon Ma'abuta Girman Kai

17:47 - November 29, 2011
Lambar Labari: 2231500
Bangaren siyasa: Hadarat Imam Khomeini a daidai lokacin da yake ganawa da shugabannin rundunar sojojin ruwa ta kasar ya bayyana karara cewa: juyin juya halin musulunci a Iran ya bawa al'ummar Iran da shugabaninta karfi da daukaka kuma Iran karkashin wannan albarka ta maidawa ma'abuta girman kai na duniya aniyarsu da kara samin daukaka.




Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ne ya watsa rahoton cewa; Hadarat Imam Khomeini a daidai lokacin da yake ganawa da shugabannin rundunar sojojin ruwa ta kasar ya bayyana karara cewa: juyin juya halin musulunci a Iran ya bawa al'ummar Iran da shugabaninta karfi da daukaka kuma Iran karkashin wannan albarka ta maidawa ma'abuta girman kai na duniya aniyarsu da kara samin daukaka. Jagoran na juyin musulunci Ayatullahil Uzma Sayyed Ali Khemenei, ya ce tun daga lokacin da al'ummar kasar Iran suka samu nasarar kawar da salon mulki na danniya da kuma dora kasar a kan turba ta musulunci ne, sojan ruwa ke taka gagarumar rawa wajen kare mutuncin Iran da kuma na al'ummarta, kuma wannan ne ya sa tun daga shekarar 1980, aka kebe ranar 7 ga watan Azar wato ranar 28 ga wa nuwambar kowace shekara a matsayin ranar sojan ruwan kasar.
Kebe wannan rana dai ya samo asali ne daga rawar zaratan sojan ruwan kasar da ake kira Peykan suka taka a lokacin kallafaffen yakin da ya barke tsakanin sabuwar jamhuriyar musulunci ta Iran da kuma gwamnatin Ba'asiyya ta Saddam Hussein mai samun goyon bayan manyan kasashen duniya a shekarar ta 1980, inda kuma sojojin ruwan na Iran suka taka rawar da ta kasance daya daga cikin dalilan durkusar da Saddam da kuma masu daure masa gindi a lokacin wannan yaki.
Su dai zaratan sojan ruwa na Peykan, su ne suka kaddamar da wani gagarumin farmaki ta ruwa wanda ya yi sanadiyyar lalata manyan cibiyoyin samar da man fetur na Al-bakr da kuma Al-Umayya da ke gabar ruwan tekun Pasha mallakar kasar Iraki, lamarin da ya girgizar gwamnatin Saddam da kuma kasashen da suka ingiza shi kaddamar da wannan yaki a kan jamhuriyar Musulunci ta Iran. Tun daga wannan lokaci ne dai aka karya lagon Saddam da kuma sojojinsa wadanda a wannan lokaci ke takama da irin goyon bayan da suke samu daga kasashen Turai da Amurka dan kawar da sabuwar gwamnatin musulunci ta Iran.
A lokacin wannan ganawa da manyan kwamandojin rundunar sojan ruwan kasar a jiya liitinin, Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullahil Uzman Sayyed Ali Khemenei, ya ce a game da irin ci gaban da wannan runduna ta sama a cikin shekarun da suka biyo bayan faruwar wannan lamari na ranar 7 ga watan Azar shekara ta 1359 hijira Shamsiyya, wannan ya sa a yau duk wani mai tunanin kai wa kasar Iran hari to dole ne ya san cewa Iran na a shirye domin mayar da mummunan martani a kansa.
Kafin jawabin na jagora, sai da babban kwamandan rundunar sojan ruwan kasar wato Admiral Sayyari ya gabatar wa jagoran da wani rahoto dangane da karfin sojan na ruwa da kuma sabbin dubaru da kuma kwarewa a fagen tsaro da rundunar ke da su a halin yanzu musamman ma a kan gabar ruwan kasar da kuma ruwan kasa da kasa.
Admiral Sayyari ya ce a cikin kwanaki 876 da suka gabata, sojan na ruwa sun gudanar da sintiri da kuma rakiyar jiragen ruwan kasar Iran da kuma na kasa da kasa domin kare lafiyarsu a kan tekun Oman, da tekun Aden, da kuma tekun Pasha, sannan kuma rundunar ta aike da wasu bataliyoyinta zuwa wasu yankuna na ruwan kasa da kasa domin fada da masu satar jiragen ruwa har sau 16.
Wata gagarumar nasarar da rundunar sojan ruwan na Iran ta sama a fagen fada da fashin jiragen ruwa kamar dai yadda babban kwamandan rundunar ya ce, akalla jiragen ruwan kasar da kuma na sauran kasashen duniya guda 40 ne ta ceta daga barazana ko kuma yunkurin fashi da tsageru ke yi a kan ruwa, kuma a sakamakon wannan kokari, rundunar ta samu yabo daga kungiyoyi da kuma cibiyoyin kasa da kasa da ke da kwarewa a wannan fage na sufurin ruwa.



907256

captcha