Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa' wani dan majalisar dokoki daga kasar Pakistan ya bayyana cewa: cibiyoyin addini da al'adu na jmahuriyar musulunci ta Iran da ke gudanar da ayyukansu a wajan Iran suna aiwatar da ayyukansu kamar yadda ya kamata da kuma dacewa kuma alasanbarka.Nasrullah Khan Darishak dan majalisar dokoki a kasar ta pakistan ya bayyana hakan ne a lokacin wani taron kan ayyukan al'adu da kuma ya kawo misali da yadda jamhuriyar musulunci ta Iran ta gudanar da gasar karatun kur'ani ga matasa a kasar ta Pakistan da cewa wannan wani abin jinjinawa da yabo ne da kuma ke zama daya daga cikin ayyukan alheri da take gudanbarwa a ketare da kuma ke zama a bin koyi ga sauran kasashe.
912698