Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: mukaddashin shugaban hukumar kula da al'adu da dangantaka a tsakanin musulmi a wata ganawa da yayi da tawagar mabiya addinin Kirsitanci daga kasar Pakistan ya bada labarin gudanar da wani gagaramin taron na tattaunawa da fahimtar juna a tsakanin mabiya addini da kuma za a samu halartar wakilan mabiya addinai daga kasashe kusan talatin da tara na duniya da kuma za a gudanar a nan gaba kasar Iran.Muhammad Rida Dahshiri ya farad a bayyana cewa; hukumar kula da al'adu da dangantaka a tsakanin musulmi da kuma kasashen musulmi wata cibiya ce ta addinai da ta kumshi masana da malamai da manazarta da kowa na iya kawo taimako da gudummuwarsa wajan kara kusanci da fahimtar juna a tsakanin mabiya addainai daban daban a duniya .Kuma matukar aka yi aiki da wannan hanya ta fahimta da tattauna a tsakanin mabiya addinai to za a kai ga barci da kawo karshen tashe-tashen hankula da rikici da sabani mai muni a tsakanin mabiya addinan.
915924