Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na na jami’ar Zaitunah cewa, j Juyin juya halin da mutanen kasar Tunisia suka yi ya baiwa masu kishin islama na kasar damar shiga a dama da su a cikin harkokin siyasar kasar da ma shiga gaba wajen jagorantar kasar a siyasarta ta yanzu kamar dai yada ake ake ganin jam’iyunsu ne suka samu nasara a zabuka.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanayin yadda lamurran siyasa ke tafiya a halin yanzu a kasar yana tabbatar da cewa an samu gagarumin canji, kuma za a ci gaba da ganin irin wannan canji a sauarn kasashen larabawa, duk kuwa da cewa kasashen yammacin turai da karnukan farautarsu daga cikin kasashen larabawa suna kokarin ganin sun juya juyin larabawa zuwa inda suke so.
Wannan juyin juya halin da mutanen kasar Tunisia suka yi ya baiwa masu kishin islama na kasar damar shiga a dama da su a cikin harkokin siyasar kasar da ma shiga gaba wajen jagorantar kasar a siyasarta ta yanzu a kasar.
922232