IQNA

An Gudanar Da Bukin Fara Gasar Kur'ani Karo na Uku A Sudan

17:22 - December 28, 2011
Lambar Labari: 2247284
Bangaren kula da ayyukan kur'ani:an gudanar da taron bukin fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai girma karo na uku a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan kuma ministan da ke kula da harkokin addini a kasar ta Sudan ne ya bude wannan gasar a dakin taro na Alsadaka da ke birnin .

Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: an gudanar da taron bukin fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai girma karo na uku a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan kuma ministan da ke kula da harkokin addini a kasar ta Sudan ne ya bude wannan gasar a dakin taro na Alsadaka da ke birnin .Wannan gasar ta fadin kasar Sudan ne kuma mahardata kur'ani dubu ashrin da daya ne za su halarci wannan gasar daga yankuna daban daban na kasar kuma za a zabi mutane goma daga cikin maza da suka fi nuna kwazo a wannan gasar sai kuma bangaren mata suma mutum goma da suka fi nuna kwarewa domin bas u kyauta ta musamman da kuma za su karbi irin kyautukan da aka yi tanadi a wannan gasar daga hannun Khalil Abdallah ministan da ke kula da harkokin addini a kasar ta Sudan.A lokacin bukin kaddamar da wannan gasar an samu halartar mutanan kasar ta Sudan masu yawan gaskiya.


923806


captcha