Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Muhammad Mahdi Hakkuguyan :ya bayyana cewa akarshen wannan wata na Dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya mahardata kur'ani mai girma za su halarci gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa da za a gudanar a kasar ta sudan.A makon karshe na wanann wata na dai ne za a fara gudanar da gasar kasa da kasa ta karatun kur'ani a kasar Sudan Shi Hakkguyan dan shekaru goma sha hudu wanda kuma yana dad an shekaru takwas ya fara harder kur'ani da kammala harder karatun kur'ani bayan shekaru biyu zai halarci wannan gasa ta kasar Sudan.
924332