IQNA

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai kan Qatar

15:38 - September 12, 2025
Lambar Labari: 3493857
IQNA - Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da wata sanarwa inda ya yi Allah wadai da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kai wa Qatar.

 jiya mambobin kwamitin sulhu na MDD sun yi Allah wadai da hare-haren baya-bayan nan da Isra'ila ta kai a birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar, tare da yin kira da a kawo karshen tashe-tashen hankula a yankin.

A cikin sanarwar da kwamitin sulhun ya fitar, mambobin kwamitin sun bayyana matukar damuwa a kan mutuwar fararen hula a wadannan hare-hare.

Sanarwar ta kuma jaddada muhimmancin kawo karshen tashe-tashen hankula da kuma goyon bayan diyaucin kasar Qatar.

A karshen sanarwar, mambobin majalisar sun sake jaddada goyon bayansu ga muhimmiyar rawar da Qatar ke takawa a kokarin shiga tsakani a yankin.

A ranar Talata, 9 ga watan Satumba, gwamnatin Isra'ila, a wani mataki da ba a taba gani ba, ta kai hari kan ofisoshin shugabannin Hamas a Doha; wani mataki da ya haifar da tarzoma a matakin yanki da na duniya. Jami'an Qatar sun bayyana harin a matsayin wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa da kuma ayyukan ta'addanci, sannan kuma da yawa daga cikin kasashen yankin sun yi Allah wadai da shi.

 

 

4304555

 

 

captcha