IQNA

19:07 - January 01, 2012
Lambar Labari: 2249343

Musulmin New York Sun Haramta Ganawa Da Magajin Garin Birnin Kan Addinai

Bangaren kasa da kasa, jagororin mabiya addinin muslunci a birnin New York na kasar sun haramta gudanar da zaman shekar-shekara da ake yi tare da magajin garin birnin inda ake tattaunawa kan harkokin addini saboda matakin da aka dauka na takura musu.




Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na canoe cewa, jagororin mabiya addinin muslunci a birnin New York na kasar sun haramta gudanar da zaman shekar-shekara da ake yi tare da magajin garin birnin inda ake tattaunawa kan harkokin addini saboda matakin da aka dauka na takura musu a cikin harkokinsu an addini da ma sauran harkokin rayuwarsu.

Bayanin y ace jagororin mabiya addinin muslunci sun koka kan yadda ake turo 'yan sanda cikin kayan sarki a wasu lokuta, a cikin masallatai domin yin bincike ta hanyar wulakci da tozarci, wasu lokuta kuma a turo jami'an liken asiri a cikin fararen kaya suna sanya ido kan dukaknin musulmi wadanda 'yan kasa ne kamar kowa.

Yanzu haka dai jagororin mabiya addinin muslunci a birnin New York na kasar sun haramta gudanar da zaman shekar-shekara da ake yi tare da magajin garin birnin inda ake tattaunawa kan harkokin addini saboda matakin da aka dauka na takura kansu.

926091




captcha