IQNA

Wakilin Ayatollah Sayyid Ali Sistani Ya Ja Kunnen 'Yan Siyasar Kasar Iraki

19:07 - January 01, 2012
Lambar Labari: 2249345
Bangaren kasa da kasa, wakilin babban malamin addinin muslunci a kasar IrakiAyatollah sayyid Ali Sistani ya gargadi 'yan siyasar kasar da su yi hattara kan matsalolin siyasar da suke fuskatar Iraki a halin yanzu a bangaren siyasa.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sautul Iraq cewa, wakilin babban malamin addinin muslunci a kasar Iraki ya gargadi 'yan siyasar kasar da su yi hattara kan matsalolin siyasar da suke fuskatar Iraki a halin yanzu a bangaren siyasa musamman ma bayan ficewar sojojin mamaya daga kasar.

A bangare guda kuma ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da bayanin taya gwamnati da al'ummar kasar Iraki murnar fitar sojojin mamayan Amurka daga kasarsu, bayanin ya kunshi cewa: Fitar sojojin mamayan Amurka daga kasar Iraki bayan tsawon shekaru takwas wata babbar nasara ce ta fuskar siyasa da tsaro ga dukkanin al'ummar Iraki.
Har ila yau bayanin yana dauke da cewa; a tsawon shekaru takwas da sojojin mamaya suka yi a Iraki, kasar ta fuskanci manyan matsaloli musamman ta fuskar siyasa da tsaro, kuma hikima da hangen nesa daga shugabannin siyasa da na addini a kasar ne suka kubutar da Iraki daga afkawa cikin yakin basasa saboda sabanin mazhaba da makiya ke rurutawa.
925852

captcha