IQNA

Yan Kasar Beljuim Za Su Fahimci Kur'ani Mai Girma

14:30 - January 02, 2012
Lambar Labari: 2249877
Bangaren kasa da kasa: al'ummar kasar Beljuim a ranar sha takwas ga watan dai na shekara ta dubu biyu da dari uku da tis'in hijira shamsiya a wani taro da za a gabatar a kasar kan kur'ani mai girma da hakikanin sakon da ke cikinsa za su samu masaniya kan kur'ani da musulunci.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa:
al'ummar kasar Beljuim a ranar sha takwas ga watan dai na shekara ta dubu biyu da dari uku da tis'in hijira shamsiya a wani taro da za a gabatar a kasar kan kur'ani mai girma da hakikanin sakon da ke cikinsa za su samu masaniya kan kur'ani da musulunci.Pagaeshalal mai kula masallacin Altauba da ke garin Evere a kasar Beljuim ya dau niyar shiryawa da gudanar da wannan taro mai taken Kur'ani mai girma da kuma gaskiyar sakon da ke cikinsa kuma za a agudanar dawannan taro ne a farkon shekara nan ta dubu biyu da goma sha biyu da muka shiga kuma burin wannan taron shi ne yin nazari da bincike da kuma fadakar da mutanan kasar ta beljuim gaskiyar sakonni da suke cikin kur'ani mai girma ga yan kasar wadanda ba musulmi ba kuma duk wani mai bukata yana iya halartar wannan taron .

926593

captcha