IQNA

Kafafen watsa Labarai na Goyan Bayan Yancin Sanya Hijabi Ga Ma'aikata Musulmi

14:28 - January 02, 2012
Lambar Labari: 2249887
Bangaren siyasa da zamantakewa; wasu daga cikin yan jarida da kafafen watsa labarai na kasar kanada sun bayyana ashirye suke su goyi bayan bawa mata musulmi dad a ke aiki a kamfanoni da masana'antu damar sanya hijabin musulunci a guraren aikinsu.




Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: wasu daga cikin yan jarida da kafafen watsa labarai na kasar kanada sun bayyana ashirye suke su goyi bayan bawa mata musulmi dad a ke aiki a kamfanoni da masana'antu damar sanya hijabin musulunci a guraren aikinsu.Gwamnatin kasar kanada ce ta ke kokarin daukan wannan mataki na fitar da wani hukumci ko doka ta bawa musulmi na kasar Mata da ke aiki a kamfanonin kasar damar sanya hijabin musulunci a guraren ayyukansu da ke ganin wannan wata dama da babban ci gaba net a fuskar hakkin dan adam da kare masa hakinsa musamman a daidai wanann lokaci na take hakkokin musulmi a kasashen yammacin turai da nuna masu karan tsana da wariya da kawo dokokin takura masu kawai don sun zabi addinin musulunci da sanya hijabi ko sitira ta kare mutunci da matsayinsu na musulmi.

926673

captcha