IQNA

Wantaren Kayan Fasaha Na Musulunci A Faransa

11:04 - January 05, 2012
Lambar Labari: 2251651
Bnagaren kasa da kasa: Artcuria a kasar Faransa a ranar ashirin ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya za ta yi wantare na kayan tarihi na fasaha na Musulunci a otel din Marcel Dassault da ke birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Artcuria a kasar Faransa a ranar ashirin ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya za ta yi wantare na kayan tarihi na fasaha na Musulunci a otel din Marcel Dassault da ke birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa.Wannan wantare za a gudanar da shi ne kashi biyu na farko kana fasaha na yammacin Turai sai kuma kashi na biyu fasaha da kayan tarihi na musulmi da za a sayar da abubuwa masu kima da daraja kamar shafukan kur'ani mai girma da aka rubuta da salon rubutu na Kufi day a samo asali da karni na goma kuma za a sayar kan kuddi tsakanin yuro dubu sha takwas zuwa ashirin da biyar .Wannan na daga cikin muhimman abubuwan da za a baje kolinsu a wannan kasuwar wantare ta fasaha .
928977
captcha