IQNA

Kasar Jordan Za Ta Cike Gurbin Husni Mubarak A Wajen Haramtacciyar Kasar Isra'ila

18:03 - January 05, 2012
Lambar Labari: 2251779
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Jordan ce za ta cike gurbin Husni Mubarak a haramtacciyar kasar Isra'ila bisa la'akari da irin gagarumar rawar da take takawa wajen biyan buktun yahudawa a cikin kasashen larabawa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, masana harkokin siyasa a cikin kasashen larabawa da yankin gabas ta tsakiya suna imanin cewa, gwamnatin kasar Jordan ce za ta cike gurbin Husni Mubarak a haramtacciyar kasar Isra'ila bisa la'akari da irin gagarumar rawar da take takawa wajen biyan buktun yahudawa a cikin kasashen larabawa a wannan lokaci.

A wani labarin kuma gwamnatin kasar Syria ta soki lamirin shishigin da gwamnatin kasar Amurka take yi a cikin ayyukan binciken da tawagar kungiyar kasashen larabawa take yi a kasar, a ranar talata da ta gabata ce gwamnatin kasar Amurka ta bayyana cewa gwamnatin Syria bata cika alkawuran da ta daukawa kungiyar kasashen larabawa kan kawo karshen rikicin da ke faruwa a kasar ba.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria Jihad Makdisi ya ce bayanin na gwamnatin kasar Amurka shishigi ne cikin lamuran kungiyar ta kasashen larabawa kuma, kasar Amurka, inji shi bata cikin tawagar da kungiyar ta aika zuwa kasar ta Syria don haka bai dace ta fadi wani abu dangane da bincikin ba sai bayan rahoton da kungiyar zata bayar nan gaba.

Bayan mako guda da fara binciken dai kungiyar zata yi wani zama a birnin alkahira a cikin mako mai zuwa don tattauna inda binciken ya tsaya ya zuwa yanzu,yan adawar kasar ta Syria dai suna zargin cewa gwamnatin kasar Syria ta karkatar da akalar tawagar binciken zuwa wasu wuraren da basu da muhimmanci.

928805


captcha