IQNA

Gasar Kur'ani Mai Girma Ta Kasa Da Kasa A Sudan

13:45 - January 10, 2012
Lambar Labari: 2254764
Bangaren kula da harkokin kur'ani: a karo na uku za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai girma ta kasa da kasa da kimanin mahardatta kur'ani daga kasashe kimanin talatin day a hada da wakilan jamhuriyar musulunci ta Iran za su halarci gasar ta birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ta watsa rahoton cewa: a karo na uku za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai girma ta kasa da kasa da kimanin mahardatta kur'ani daga kasashe kimanin talatin day a hada da wakilan jamhuriyar musulunci ta Iran za su halarci gasar ta birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan. Wannan gasar karatun kur'ani mai girma kungiyar kula da harkokin kur'ani mai girma a kasar ta sudan ta dauki nauyin gudanarwa da kuma za a kwashe tsawon mako guda ana gudanarwa da kuma za a fara a ranar litin mai zuwa ashirin da shidda ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya da kuma za a kawo karshen gasar a ranar biyu ga watan Bahman .Kimanin makaranta kur'ani dari biyu da hamsin ne za su fafata da juna da suka fito daga kasashen musulmi irin su jamhuriyar musulunci ta Iran,Suriya,Koweiti, Saudiya, Turkiya, Masar,Libiya,Katar,Tunusiya,Etiophiya,Afrika ta kudu,Chadi, Senegal, da sauran kasashen musulmi.
931658

captcha