Bangaren kasa da kasa, cibiyar kula da ayyukan raya harkokin al’adu da na addinin muslunci a yankin palastine ta sanar cewa sojojin haramtacciyar kasar Isra’ia sun kai wani samame kan al’ummar yankin a cikin masallacin Qods mai alfarma.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na Palestine cewa cibiyar kula da ayyukan raya harkokin al’adu da na addinin muslunci a yankin palastine ta sanar cewa sojojin haramtacciyar kasar Isra’ia sun kai wani samame kan al’ummar yankin a cikin masallacin Qods mai alfarma a daren jiya a lokacin da ake gudanar da salla.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan ba shi ne karon farko da aka ga sojojin yahudawan sahyuniya suna kai irin wannan farmaki ba, lamarin da ya tunzura mutane da fusata su, amma dai ba biye musu ba wajen yin bata kashi ba.
Babbar cibiyar kula da ayyukan raya harkokin al’adu da na addinin muslunci a yankin palastine ta sanar cewa sojojin haramtacciyar kasar Isra’ia sun kai wani samame kan al’ummar yankin a cikin masallacin Qods mai alfarma a cikin makon jiya.
Hatamtacciyar tana da shirin gina wasu dubban matsugunnan yahudawa ‘yna kaka gida acikin yankunan palastinawa da ke gabacin birin Qods, duk kuwa da kiran da kasashen yammaci suka yi da a guji hakan.
931700