IQNA

12:46 - January 15, 2012
Lambar Labari: 2257030

Yin Kisan Gilla Kan Masana Harkokin Nukiliya Na Iran Ba Zai Tsayar Da Shirinta Ba

Bangaren kasa da kasa, yin kisan gilla kan masana harkokin nukiliya na kasar ba iya tsayar da shirinta na makamashin nukiliya da take gudanarwa ba kamar yadda makiya suke zato.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-manar cewa, babban sakataren kungiyar gwagwamaya ta Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa yin kisan gilla kan masana harkokin nukiliya na kasar ba iya tsayar da shirinta na makamashin nukiliya da take gudanarwa ba kamar yadda makiya suke zato sakamakon abin da suke yi yanzu a kasar.

A bangare guda kuma Iran ta danganta kisan gillar da ake yi wa masananta kan harkokin nukiliya da bayanan da ta baiwa hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya kan shirinta.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Ramin Mehman Parast ne ya bayyana hakan a jiya, inda ya ce dukaknin masanan da aka yi wa kisan gilla suna daga cikin wadanda Iran ta bayar da sunayensu ga hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, wanda kuma an yi hakan ne bisa yarjejeniya tsakanin Iran da kuma hukumar, kamar yadda kaidoji na kasa da kasa suka shata, amma abin mamaki ne yadda ake bin wadannan masana daya bayan daya ana yi musu kisan gilla, ya ce hakan ya sanya Iran yin shakku kan amincin hukumar kula da makashin nukiliya ta duniya.

A nasa bangaren masani kan harkokin siyasa a kasar Amurka John Parker ya fadi a wata zantawa da ta hada shi da gidan talabijin presstv a daren jiya cewa, yin kisan gilla kan masana harkokin nukiliya kasar Iran, na daga cikin abubuwan da hukumar leken asiri ta Amurka CIA, da kuma kungiyar liken asiri ta HKI suka mayar da hankali kansu. 934718
captcha