IQNA

An Gudanar Da Tarukan Cika Shekara Guda Da Juyin Juya Halin Kasar Tunisia

15:32 - January 16, 2012
Lambar Labari: 2257949
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da tarukan cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Tunisia tare da halartar dubban daruruwan mutane da suka gudanar da zanga-zangar goyion baya ga juyi da kuma yin Allawadai da halaratr sarkin Qatar a wurin.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo harun yahya.fr cewa, an gudanar da tarukan cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Tunisia tare da halartar dubban daruruwan mutane da suka gudanar da zanga-zangar goyion baya ga juyi da kuma yin Allawadai da halaratr sarkin Qatar a wurin wadannan taruka.
A jiya ne aka gudanar da tarukan cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Tunisia, wanda ya kawo karshen mulkin kama karya na tsohon shugaban kasar Zainul Abidin Bin Ali.
Mai aiko ma gidan talabijin Al-alam rahotanni daga kasar Tunisia ya habarta cewa, a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan a hukumance a birnin Tunis, dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a wasu biranan kasar, inda suka yi Allawadai da ziyarar sarki Qatar a kasarsu, wanda yake halartar bukukuwan cika shekara guda da samun juyi a kasar.
Dubban masu zanga-zanga a birnin Saqas na kasar Tunisa, sun daga kyallaye da kwallaye da aka rubuta cewa, sarki Qatar Karen farautar Amurka da yahudawa ne, saboda haka al'ummar Tunisia ba su lalae marhabin da shi a kasarsu.
935170

captcha