IQNA

Ban Ki Moon Ya Yi Allawadai Da Kashe Masanin Harkokin Nukiliya Na Iran

15:30 - January 16, 2012
Lambar Labari: 2257953
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya yi kakkausar suka da yin Allawadai da kisan gillar da aka yi masanain harkokin nukiliya na kasar Iran a cikin wannan mako tare da bayyana hakan da cewa aiki ne na ta’addanci.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na tashar talabijin din Russia Today cewa, babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya yi kakkausar suka da yin Allawadai da kisan gillar da aka yi masanain harkokin nukiliya na kasar Iran a cikin wannan mako tare da bayyana hakan da cewa aiki ne na ta’addanci da ba za a taba amincewa da shi ba.
A nata bangaren gwamnatin Iran ta danganta kisan gillar da ake yi wa masananta kan harkokin nukiliya da bayanan da ta baiwa hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya kan shirinta.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Ramin Mehman Parast ne ya bayyana hakan a jiya, inda ya ce dukaknin masanan da aka yi wa kisan gilla suna daga cikin wadanda Iran ta bayar da sunayensu ga hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, wanda kuma an yi hakan ne bisa yarjejeniya tsakanin Iran da kuma hukumar, kamar yadda kaidoji na kasa da kasa suka shata.
Ya ce amma abin mamaki ne yadda ake bin wadannan masana daya bayan daya ana yi musu kisan gilla, ya ce hakan ya sanya Iran yin shakku kan amincin hukumar kula da makashin nukiliya ta duniya.
A nasa bangaren masani kan harkokin siyasa a kasar Amurka John Parker ya fadi a wata zantawa da ta hada shi da gidan talabijin presstv a daren jiya cewa, yin kisan gilla kan masana harkokin nukiliya kasar Iran, na daga cikin abubuwan da hukumar leken asiri ta Amurka CIA, da kuma kungiyar liken asiri ta HKI suka mayar da hankali kansu.
934871



captcha