Bangaren kasa da kasa, gungun matasa masu gudanar da zanga-zangar nemna sauyi a cikin kasar Bahrain sun bayyana cewa sarkin yana kokarin gudu daga bukatun jama'a ta hanyar sanar da cewa yana son yin gyara a cikin harkokin mulkin kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-wifaqh cewa, gungun matasa masu gudanar da zanga-zangar nemna sauyi a cikin kasar Bahrain sun bayyana cewa sarkin yana kokarin gudu daga bukatun jama'a ta hanyar sanar da cewa yana son yin gyara a cikin harkokin mulkin kasar musamman ma ganin yadda al'umar kasar suke ci gaba da nuna rashin gamsuwa da salon mulkinsa.
Babban sakataren jam'iyyar Al-Wifaq ta kasar Bahrain ya sake jaddada matsayar jam'iyyar da sauran al'ummar kasar na ci gaba da zanga-zangar da suke yi wajen ganin an haifar da sauyi na siyasa a kasar.
A wata tattaunawa da ya yi da tashar talabijin din Al-Manar ta kasar Labanon Sheikh Ali Salman babban sakataren jam'iyyar Al-Wifaq din har ila yau ya yi watsi da sauyin da sarkin kasar Bahrain din ya yi alkawarin yi a cikin kundin tsarin mulkin kasar yana mai cewa hakan wani kokari ne kawai na tabbatar da mulkin kama-karyar da gidan sarautar Bahrain.
A shekaran jiya ne dai sarkin na Bahrain ya yi alkawarin haifar da sauyi a cikin kundin tsarin mulkin kasar lamarin da dadama daga cikin al'ummar kasar suke ganin hakan a matsayin wani kokari na wasa da hankalin al'ummar kasar kawai.
935930