Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Darik Ramadan masanin addinin musulunci kuma marubuci malamain jami'a a jami'ar Aksford shi ne aka zaba a matsayin sabon shugaban cibiya ta kasa da kasa mai kula da bincike da nazari a harkokin da suka shafi kyawawan dabi'u da dokokin musulunci a Katar.an jiyo daga jaridar Safir News a kasar katar cewa; Darik Ramadan da Jasir Auda an zabe su a matsayin shugabannin wannan cibiya kuma wannan it ace cibiya ta farko irinta a duniya musulmi da aka kafa ta a ranar ashirin da biyar ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a kasar Katar da kuma za ta rika sa ido kan abubuwa da suka shafi kyawawan dabi'u da dokokin na addinin musulunci.
938262