Kamfanin dillancin labarai na ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; mukaddashin jam'iyar islami a jamhuriyar azarbaijan a wani zaman kotu a garin Sumaka'it na wannan kasar an tyanke masa hukumci tsare shi a gidan yari na tsawon shekaru biyu da watannin shidda.Wannan hukumci da kuma zargin da ake yi masa da bai taka kara ya karya ba yana nuni da yadda ake take hakkin musulmi da shugabanninsu a wannan kasa da kuma gwamnati da mahukumta a wannan kasa ke tsananta daukan hukumci kan musulmi da jam'iyu da kungiyoyin musulmi da kuma uwa uba shugabanninsu kan wani laifi da bai taka kara ya karya ba yayin da ake nuna halin ko in kula kan lamarin day a shafi musulmi da kuma nuna sausauci kan masu adawa da musulmi da kungiyoyinsu.
941673