Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alkhalij cewa, babban kwamitin shirya gasa ta karatun kur’ani da kuma harda a kasar hadaddiyar daular larabawa ya sanar cewa an kammala dukaknin shirye-shiryen da suka kamata domin gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya kamar dai yadda aka saba gudanarwa a kasar a kowace shekara.
Bayanin ya ci gaba da cewa gudanar da irin wannan taro na gasar karatun kur’ani a kasar ta haddaiyar daular larabawa na daga cikin abubuwan da akan gudanar shekara-sheakara a garuruwa daban-daban na kasar, inda awannan karon za agudanar da wannan taron a garin Ra’asulkhaimah.
Babban kwamitin shirya gasa ta karatun kur’ani da kuma harda a kasar hadaddiyar daular larabawa ya sanar cewa an kammala dukaknin shirye-shiryen da suka kamata domin gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya, da aka saba gudanarwa akasar hadaddiyar daular larabawa.
942447