Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shfin sadarwa na yanar gizo na egynews cewa, a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon an gudanar da wani zaman taro domin nuna cikaken goyon baya ga masallacin Qods da wurare masu alfarma da suke cikin birnin tare da yin Allawadai da haramtacciyar kasar Isra’ila kan tozarta wurare masu tsarki da suke cikin wannan birni.
Haka nan kuma an habarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin dil Almanar cewa, ana shirin gudanar da wani shiri da aka kira da yunkurin nuna goyon baya ga masallacin Qods ta hanayar sadarwa wanda hakan shi ne karon farko da masana a wannan bangaren za su gudanar da irin wannan shiri.
Kungiyar kasashen musulmi ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da haramtacciyar kasar Isra’ila kan harin ta’addancin da ta kai masallatan musulmi palastina a cikin yankunan gabar yamma da kogin Jordan a cikin wannan mako.
Yanzu haka dai haramtacciyar kasar Isra’ila na ci gaba da gudanar da ayyukanta na ta’addanci tare da cikakken goyon bayan Amurka da kasashen, yayin da larabawa suka shagaltu da kokarin kawar da gwamnatocin da ke kawo Isra’ila cikas.
942756