IQNA

Dan Majalisar Dokoko A Labanon Ya Taya Murna Da Zagayowar Nasarar Juyin Juya Halin Musulunci

16:26 - February 06, 2012
Lambar Labari: 2269822
Bangaren kasa da kasa: Said Huseni Almusawi manba a komitin sadaukarwa da gwagwarmaya majalisar kasar Labanon ya taya gwamnatin jamhuriyar musulunci ta Iran da kuma al'ummar kasar iran murnar zagayowar ranekun nasarar juyin juya halin musulunci da Iran ta samu karkashin jagorancin mu'assasin juyin Imam Khomeini .



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Said Huseni Almusawi manba a komitin sadaukarwa da gwagwarmaya majalisar kasar Labanon ya taya gwamnatin jamhuriyar musulunci ta Iran da kuma al'ummar kasar iran murnar zagayowar ranekun nasarar juyin juya halin musulunci da Iran ta samu karkashin jagorancin mu'assasin juyin Imam Khomeini . Gidan talbijin din Almanar ne da ke watsa shirye-shiryensa ta hanayr tauraron dan adam daga kasar labanon ya watsa bayanin na wannan dan majalisar dokoki na kasar Labanon Said Husein Almusawi da ke jinjinawa mahukumtan jamhuriyar musulunci na baya da suka jagoranci wannan gagaramin juyin day a kai ga nasara da a yau al'ummar Iran na wancan lokaci da kuma a l'ummar Iran nay au da sauran takwarorinsu na duniya suke cimma moriyar wannan nasara ta juyin juya halin musulunci, Ya ci gaba da cewa yau shekaru talatin da uku ken an da samin wannan nasara ta juyin juya halin musulunci a Iran da hakan ke zama babban nasar ga al'ummomin duniya musamman ya gwagwarmaya daga cikinsu da kuma masu son yanci da adalci ya wanzu a fadin duniya da kuma samar da yanayi na rayuwa mai inganci da walwala.


947361
captcha