Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, mataimaki shugaban majalisar hada kan mazhabobin muslunci ya sheda cewa, hadin kan al'ummar msuulmi ya zama wajibi kamar yadda dama wajibi ne, amma a wannan zamanin da musulunci da musulmi suke fuskantar barazana daga makiya wajabcin yafi karfi fiye da kowane lokaci domin tunkarar gagarumin aikin aikin da ke gaban wannan al'umma.
Bayanin ya ci gaba da cewa a wani labarin kuma mataimakin babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin muslunci a Iran Janar Hussain Salami ya jaddada cewa duk kasar da ta baiwa makiya dammar yin amfani da kasarta don kaddamar da hari kan Iran, to suna kallon wannan kasar a cikin jerin makiya.
A cikin wani jawabi da yagabatar jiya a gaban manema labarai a birnin Tehran, janar Salami ya sheda cewa dakarun kare juyin juya halin muslunci suna ci gaba da gudanar da atisayinsu a kudancin kasar Iran, domin tabbatar da cewa sun kamala duk wani shiri na fuskantar kowace irin barazana daga kasashe makiya, ya ce idan makiyan Iran suka yi amfani da wata kasa domin kai hari a cikin Iran, to dakarun kare juyin juya halin muslunci ba su yi wata-wata ba wajen mayar da mummanr martani a kan wannan kasar.
A cikin 'yan lokutanan nan dai Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila, suna ta nanata barazanar kaddamar da harin soji kan tashoshin nukiliyar Iran. Lamarin da Iran din ta ce ba shayi a kansa.
947693