Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-alam cewa, a wata zantawa da ta hada talabijindin da babban sakataren kwamitin kusanto mazhabobin addinin muslunci na duniya Aytaollah Muhammad Ali Taskhiri ya jaddada wajabcin fadakar al'ummar musulmi dangane da makircin da ake shirya musu domin kara rarraba kawunansu da kuma kawo rikici mai muni a tsakaninsu.
Irin abubuwan da suke faruwa a wasu kasashe da aka samu juyi manuniya ce kan wannan dasisa, inda dauki ba dadi tsakanin masu zanga zangar neman kawo karshen mulkin soji a Masar da jami'an tsaron kasar ya lashe rayukan mutane akalla 12 tare da jikkata fiye da 2500.
A ci gaba da dauki ba dadin da ake yi kwanaki uku a jere a kasar Masar tsakanin masu zanga zangar neman kawo karshen mulkin soji da jami'an tsaron kasar, gumurzun ya lashe rayukan mutane akalla 12 tare da jikkata wasu fiye da na daban.
Jami'an tsaron kasar ta Masar suna amfani ne da iskar gas mai sanya hawaye da nufin tarwatsa masu zanga zangar, yayin da masu zanga zangar ke ruwan duwatsu ga jami'an tsaron.
A gefe guda kuma masu zanga zangar suna zargin jami'an tsaron kasar da harbi da bindiga, sannan tarzomar jama'a ta kai ga kona wani ofishin 'yan sanda gabashin birnin Alkahira.
Dauki ba dadi tsakanin masu zanga zangar neman kawo karshen mulkin soji a Masar da jami'an tsaron kasar ya lashe rayukan mutane akalla sha biyu tare da jikkata fiye da dubu biyu.
947663